<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>409</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Ga Allah kaɗai, Mahiliccinmu,
 Daidai mu yi waƙar yabonsa yanzu.

[V2]
 KORUS
 Mu yi waƙar yabon Allah
 Addu'ar za mu yi.
 Mu yi waƙar yabon Allah,
 Mu girmama shi.

[V3]
 2) Mu girmama shi, addu'ar za mu yi.
 Mai kyauta ba gori duk baiwa sai shi.
 Korus

[V4]
 3) Mai raya mutum kyautar, Allah sosai
 Ban da Allah, ina za mu sami jinƙai?
 Korus

[V5]
 4) Jinƙai ne ya sa ya yi mana baiwa
 Da ya aiko Mai Ceto tun zamani dā.
 Korus

[V6]
 5) Mai Ceto ne shi wanda Allah ya ce
 Shi Ɗansa ne, ransa ya so shi sarai.
 Korus

[V7]
 6) Labarin Mai Ceto da daɗi ya ke
 Mutuwassa da tashinsa duk namu ne.
 Korus

[V8]
 7) Duk wanda ya ce Almasihu zai bi,
 Tsattsarken numfashi zai ƙarfafa shi.
 Korus</lyrics>
<title>Ga Allah Kaɗai, Mahiliccinmu LW409</title>
</song>